Me ka ke nema?


Shafin Farko

Gidan Nassarawa



Filin Gidan Sarkin Kano Na Nassarawa


Gida ne na sarauta da sarkin Kano Abdullahi Ɗan Dabo ya gina shi a 1966. Asalin kafuwar wannan gida shi ne cewa wata rana sarki ya yi hawan kilisa, ya fita zuwa Dutsen Magwan. Da ya isa can sai ya gangara zuwa Kudu da dutsen sai ya shata wani fili sannan ya umarci sarkin gininsa da a gina masa gida a wannan waje har ma ya sake nuna gurbin da za a gina masa masallaci a gaban gidan.


Fuskar Gidan Sarkin Kano Na Nassarawa

Tun daga wannan rana aka fara gini gadan-gadan har sai da aka ɗauki tsawon watanni shida sannan aka kammala. Bayan an kammala aka sanar da sarki, sarki ya yi hawa ya je ya buɗe wannan gida nasa.


Masallacin Gidan Sarkin Kano Na Nassarawa

A kan hanyar sarki ta dawowa gida, sai ya shigo ta ƙofar da ya fita, wacce a wancan lokacin ake kiranta da ƙofar Ƙawaye. Da ya dawo sai ya ce daga wannan rana a riƙa kiranta da Ƙofar Nassarawa.

Manazarta:


Ziyarar gani da ido a ranar 24/01/2019.


Sauran Shafukanmu:

Rumbun Ilimi   Maidarasu    Balangada    Tashar Yutub